Jiki Magayi: Gwamnoni Sun Gane Kuskure Ne Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Mohammed

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, Fadar Shugaban kasa ta ce gwamnoni sun gane kuskurensu na yin sulhu da ƴan fashin daji masu satar mutane a jihohin arewa maso yammacin ƙasar.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wani shirin safe (Good Morning Nigeria) na kafar talabijin ɗin NTA na ranar Talata.

Ministan ya ce gwamnoni ba su gane cewa bai kamata su yi sulhu da ƴan bindiga ba, inda yanzu suka fahimci kuskurensu.

“Gwamnonin sun koyi darasi daga kura-kuran da suka faru a baya kuma sun yanke shawarar cewa ba za su tattauna da ‘yan fashi ba sai dai su fatattake su,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa yanzu ne gwamnonin suka ɗauki matakan da suka dace na magance matsalar ƴan bindigar.

A cewar Lai Mohammed, matakan katse hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwannin mako da hana sayar da baburan da sayar da man fetur suna aiki a yanzu.

Ya ce an toshe hanyoyi da dama da ke da alaƙa da ƴan bindigar, musamman katse hanyoyi na mu’amularsu ta samun bayanai da abinci.

Sai dai ministan yaɗa labaran na Najeriya wanda ya ce matsalar ƴan fashin daji matsala ce da ta shafe tsawon shekaru 10 a Najeriya, ya ce halin da matsalar ta jefa ƙasar ba batu ba ne na yanzu.

Lai Mohammed ya ɗora laifin ruruwar matsalar ga rashin shugabanci nagari.

Amma ya yaba wa gwamnonin yankin arewa maso yammaci waɗanda ya ce yanzu sun haɗa kansu domin tunkarar matsalar.

Ministan ya kuma bayyana matsayin gwamnatin Najeriya kan ce-ku-ce-ku-ce da ake kan batun ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda.

Ƴan majalisar dokokin ƙasar ne suka buƙaci gwamnatin Buhari ta ayyana ƴan fashin dajin da suka addabi yankin arewa maso yammaci a matsayin ƴan ta’adda.

Lai Mohammed ya ce matakan soji da gwamnatin tarayya ke ɗauka kan masu aikata laifi ba wai ana bambancewa ba ne tsakanin ƴan fashi da ƴan ta’adda.

“Mai laifi, mai laifi ne, ko da ɗan fashi ne ko ɗan ta’adda kuma matakai ɗaya ake ɗauka akansu.”

“Shi ya sa muke ganin abin dariya ne, kan sukar da ake yi wa gwamnatin tarayya cewa tana yi wa ƴan fashi sassauci fiye da ƴan a ware da sauran masu aikata laifi.”

“Wannan labaran ƙarya ne da yaɗa bayanan da ba su dace ba, da wasu masu yaɗa labaran ƙage da ƙarya suke yaɗawa,” in ji shi.

Lai Mohammed ya ƙara da cewa “rashin hankali ne ace waɗanda ke kashe sojoji da ƴan sanda a ace ana masu sassauci.”

Ya ce tsarin sojoji na yaƙi da masu laifi ba ya da wani bambanci tsakanin ƴan fashi da sauran masu aikata laifi.

Ministan ya ce sabbin matakan da gwamnonin jihohin da ƴan fashi suka addaba suka ɗauka na ba sani ba sabo , ana samun nasara.

Ya ce tun farko kamata ya yi a fita a kakkabe su kuma abin da ya faru ya zama darasi a yanzu, domin gwamnoni sun dauki matakan da suka dace.

Labarai Makamanta

Leave a Reply