Jihar Ribas: Ana Zaman Ɗar-Ɗar Sakamakon Harin Da Aka Kai Wa Hausawa

Mutane biyu ake zargin sun mutu a garin Oyigbo ta jihar Ribas bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne su ka kai masu hari.

An hallaka wadannan Hausawa ne a inda su ke zama a karamar hukumar Oyigbo kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafin ta na yau litinin 7 ga watan satunba.

Wani wanda abin ya faru a gabansa, ya ce miyagun ‘yan kungiyar IPOB sun aukawa wadannan Bayin Allah ne a ranakun Asabar da Lahadi da su ka gabata. Bayan mutum biyu da aka kashe, ana zargin an yi wa akalla wasu mutum biyu mummunan rauni.

“ Wannan shaida ya kara da cewa: “An ce an kashe mutum biyu a harin, yayin da wasu biyu su ka gamu da rauni sosai.” Mai magana da yawun mutanen Arewa da ke zaune a Ribas, Alhaji Musa Saidu, ya tabbatarwa ‘yan jarida da aukuwar wannan labari maras dadi. Alhaji Musa Saidu ya ce wasu tsageru da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne sun kai wa mutanensu hari a karamar hukumar Oyigbo, har kuma aka rasa rayuka. Kakakin kabilun Arewan ya ce a ranakun Asabar da Lahadi ne wadannan matasa su ka shiga yankin Oyigbo inda ake da tarin Hausawa a yankin dauke da makamai.

” Alhaji Saidu ya ce an kashe Hausawa biyu da su ke kananan kasuwanci a garin, sannan an bar wasu biyu da munanan raunuka kamar yadda wata majiya ta tabbatar. Mutanen Arewan sun yi kira ga jami’an tsaro su binciki wannan ta’adi amma har yanzu ba a san abin da ya kawo wannan kisa ba domin haryanzu ba aji ta bakin ‘yan sandan jihar Ribas ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply