A daren jiya masu garkuwa da jama’a suka je har gida suka yi awon-gaba da Alhaji Surajo Body a garin Garki dake jihar Jigawa.
Haƙiƙa wannan bawan Allah mutum da ya yi suna sannan ya ciri tuta ta fuskar tallafawa al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi, ko a hanya kuka haɗu dashi idan rabonka ya rantse sai ya yi maka kyautar da sai ka sha mamaki.
Mutane da yawa sun yi ittifaƙin duk cikin kwaryar garin Garki babu mutum mai taimako sama da shi.
Dan haka, muke roƙon ƴan uwa na kusa dana nesa dasu saka wannan bawan Allah a cikin addu’o’insu domin Allah ya kuɓutar dashi cikin Salama da kwanciyar hankali.