Jigawa: Sanata Ahmed Malam Madori A Tarihi Ya Fi Kowa Taimakawa Karatun Gaba Da Sakandare

Daga Ahmed Ilallah

Duk da cewa a nawa ra’ayin kamata yayi wakilan al’ummah musamman a Majalissar Dokoki su maida hankali wajen samar da doka da kuma tilastawa shugabannin wajen samar da yanayi mai kyau da duk Dan Talaka zai samu kowane irin ilimin da yake da burin samu.

Dagewa da tilastawa gwamnati wajen sanya kudin makarantu dai dai da aljihun dan talaka.

Sam ban gamsu da maida bada gudun mawa ko tallafi ga dalibai ba ya zama abun gasa tsakanin shugabanni.

Wannan tsari ba komai ya ke ingizawa ba sai mutuwar zuciyar matasan mu, da kuma jawowa shugabannin bakin jini da adawa a wajen wasu matasan da irin wannan dauni bai kai musu ba.

Amma duk da haka a tarihin bada irin wannan gudunmawa, Senator Ahmed Malam Madiro yafi kowa bada gudunmawar tallafawa yara masu karatu na gaba da sakandare.

Ko a baya nayi wani rubutu a kan hallin rashin isassun ma’aikatan jinya a yankin da irin kokarin kaiwa matasa da yake makarantun koyan aikin jinya.

Duk da cewa, wadanda su rike wannan kujera a baya sun yi irin tasu gudumawar a kan harkar ilimi a wannan yankin.

A misali tsohon Senata Ubali a zamanin sa ya yi kokarin biyawa yara kudin jarabawar JAMB da kuma gyaran jarabawar sakandare.

Tsohon Sanata Ibrahim Hadejia a zamanin sa ya maida hankali wajen karatun yara da yaya mata, yayin da ya rabawa yara mata kekuna a shirin sa EDUKEKE da kuma shirya gasa da bada kyautu ga yara yan basic schools.

Amma Senator Ahmed tun kafin zaman sa sanata yake tallafa wa wajen biya wa yara kudin registration da kuma tallafawa su koma makaranta. Biyawa yara kudin makaranta ba sabon abu bane a wurin sa.

Senator Ahmed Malam Madori ko a watan da ya gabata ya biyawa yara kusan guda gome domin zuwa karatun aikin jinya. A wannan lokacin ma da ya bawa daliabai masu karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano gudunmawa.

Duk wanda yaje kusa da wannan Senatan zai fahimci burinsa da damuwar sa wajen gannin yaran mu suna tafiya karatu, kullum burin sa ya taimake su.

alhajilallah@gmail.com (+234 8025 951 609 text only)

Labarai Makamanta

Leave a Reply