Alummar mazabar ?an Majalisar Wakilai ta ?asa mai wakiltar ?ananan hukumomin Birnin Kudu/Buji dake jihar Jigawa, Magaji Dau, sun nuna fushinsu ga ?an majalisar inda suka kai wa tawagarsa hari a garin Kukuma akan hanyarsa ta zuwa taron siyasa.
Alummar maza?ar sun zargi ?an majalisa Dau da yin watsi dasu da tarewa a Abuja na tsawon lokaci.
Yan sanda sun shaida wa wakilinmu cewa ?an majalisar yana kan hanyarsa ta zuwa wani taron siyasa ne a yankin lokacin da abin ya faru.
Maimagana da yawun Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce ba yan bindiga ne suka kai harin ba, rashin fahimta ce kawai tsakanin wasu ?angarorin siyasa ya haifar da harin.
An shawo kan alamarin kuma ?an sanda sun kama wa?anda ake zargi, in ji Lawan.
Maharan sun tare hanyar da ?an majalisar zai je ?auyen Kukuma don halartar wani taron siyasa.
Alummar maza?ar Dau sun yi ta jifar sa da munanan kalamai, suna masu zargin sa da rashin yin kata?us da kuma watsi da su har sai yanzu da za?en 2023 ya kusa.
Siyasa ta kunno kai yanzu, mutane na nan suna kakkabe katin za?en su. Wasu za su sha wasu kuma yadda hali ta yi.
Da yawa daga cikin ?an siyasa sukan wancakalar da mutanen maza?un su ne idan suka ci za?e sai kuma lokacin neman ?uriun su yayi sai su fara lekowa gida akai akai suna sharar fage.