Jigawa: Manomi APC Za Ta Tsayar Gwamna A 2023 – Badaru

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya ce ya zama dole ga ‘dan takarar gwamna a 2023 ya kware a harkar noma.

Gwamna Badaru ya kara da cewa duk wanda zai rikewa jam’iyyar APC a zaben 2023 a jihar Jigawa, sai ya zama ya na da ilmin aikin gona.

Jaridar Tribune ta rahoto gwamnan yana wannan jawabi ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2020, a karshen makon nan.

Gwamna Badaru ya jagoranci shuka itatuwa a garin Garki da ke jihar Jigawa, inda a nan ya yi magana game da wanda zai gaje shi.

A cewar Gwamna Badaru, jihar Jigawa ta dogara da noma, ya kamata duk wanda zai yi mulki a jihar ya zama ya lakanci aikin noma domin kawowa al’umma cigaba.

Gwamnan bai bayyana sunan wani dan siyasa da ya ke ganin ya fi dacewa da zama gwamna a 2023 ba, sai dai kawai ya ba sanin harkar noma Muhimmanci, Ya Kara Da Cewa JiharJigawa tana da filin noma wanda mutane zasu iya yin shuka har sau uku a cikin shekara guda.

Gwamna Badaru Ya Kara Da Cewa Hanyar da za a bi wajen bunkasa noma shi ne inganta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply