Babbar kotun majastire dake zaman ta a Dutse babban birnin jihar Jigawa, ta yankewa matashi Sabiu Ibrahim Chamo hukuncin daurin wata shida a gidan kurkuku sakamakon wasu kalaman bata suna da yayi ga gwamna Badaru Abubakar Talamiz.
Matashin, wanda ya wallafa a shafin sa na Facebook cewar; gwamnan ya karbi kudin mutane da yawa dan ya basu takara anma daga karshe ya wofantar da su, zargin da matashin ya kasa karewa da hujja, a don haka kotu ta same shi da laifi.
Kotu ta kuma daure matashin na tsawon watanni 6 a gifan kurkuku ko kuma zabin biyan tarar naira dubu 20 tare da Bulala 20 ta je ka gyara halin ka.