Jigawa: An Tsare Makahon Da Ya Yi Yunkurin Luwaɗi Da Ɗan Jagoranshi

Wata kotun majistare da ke garin Dutse a jihar Jigawa a ranar Laraba, ta bada umarnin adana mata wani makaho mai shekaru 60 mai suna Muhammad Abdul a gidan kaso.

Ana zarginsa da yunkurin yin luwadi da dan jagorarsa, lamarin da yasa aka bukaci adanasa a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun majistaren mai suna Akilu Isma’il, wanda ya umarci a adana masa Abdul a gidan gyaran halin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.

‘Yan sandan sun gurfanar da Abdul, wanda ke zama a karamar hukumar Guru ta jihar Yobe, sakamakon zarginsa da yunkurin aikata mugun aikin.

Tun farko, babban lauyan mai gurfanarwa, Kabiru Warwade, ya sanar da kotun cewa Abdul ya aikata laifin a ranar 8 ga watan Satumba wurin karfe 10 na safe a kwatas din Garko da ke karamar hukumar Hadejia.

Warwade ya ce Abdul ya ja yaron zuwa dajin da ke bayan kotun Shari’a da ke Hadejia, kuma ya yi yunkurin luwadi da shi. Dan sanda mai gabatar da karar ya ce, hakan ya ci karoo da tanadin sashi na 95 na dokokin Penal Code.

Labarai Makamanta