Jigawa: An Cigaba Da Saurarar Shari’ar Tsohon Gwamna Saminu Turaki

Rahotannin dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar an cigaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse babban birnin jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu.

An ruwaito Saminu Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan a Baitul Malin Gwamantin Jihar.

A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta damke tsohon gwamnan kuma ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari’a Binta Murtala Nyako.

Daga bisani an garkame shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da aka bayar da belinsa kan kudi naira miliyan dari tare da ‘yan majalisar tarayya biyu, Bawa Bwari da Bashir Adamu, a matsayin tsayayyunsa.

A shekarar 2011, an mayar da shari’ar babbar kotun tarayya da ke Dutse bayan wanda ake zargin ya soki cewa kotun babban birnin tarayya ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

An sake gurfanar da shi a gaban kotun kan zargin aikata laifuka 32 a Dutse. Mai shari’a Hassan Dikko aka mika wa shari’ar bayan Mai shari’a S. Yahuza ya yi ritaya.

An cigaba da sauraron shari’ar a Dutse a ranar 7 ga watan Disamban 2021 bayan ajiye shari’ar da aka yi na tsawon shekaru. Bayan wannan cigaban, wanda ake zargin kuma tsohon gwamnan ya musanta aikata laifukan 32 da ake zarginsa da su.

Mai shari’a Dikko ya saka ranakun 24 da 25 na watan Fabrairun shekara mai zuwa domin cigaba da shari’ar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply