Jigawa: Ambaliyar Ruwa Ya Ci Rayuka 92

Rahoton dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar yawan wadanda ambaliyar ruwa yayi ajalinsu a jihar ya haura sama inda ya kai har mutum 92.

Wannan yana zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yake shan caccaka sakamakon shillawa kasar waje da yayi hutu ba tare da ziyartar wadanda ibtila’in ya fadawa ba.

Kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Lawan Adam, ya tabbatar da cewa mutum 92 suka rasa rayukansu tsakanin watan Augusta zuwa Satumba sakamakon ambaliyar ruwa.

Lawal Adam ya sanar da manema labarai a ranar Litinin cewa, da yawa daga cikin wadanda suka mutu ruwa ne ya tafi da su, ko tsawa ko kuma gini ya ruso musu.

An ruwaito cewa dubban gidajen kasa, gadoji da tituna duk suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan, lamarin da yasa jama’a suka dinga tururuwar komawa sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.

A makon da ya gabata, wasu daga cikin wadanda suka koma sansanin ‘yan gudun hijira a fadin jihar sun koka kan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula garesu. Sun ce ba a samar musu da kayan rage radadi ba da na kiwon lafiya, sun yi ikirarin cewa wasu daga cikin matan sun haihu a wurin ba tare da likitoci sun duba su ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply