Jiga-jigan jam’iyyar APC da ke tsammanin samun mukaman siyasa, musamman wadanda suka yi aiki wajen zaben Shugaban kasa Bola Tinubu sun shiga rudani, inda suka kaji da jiran gawon shanu har yau ba su sami mukami ba a wannan gwamnatin.
Daya daga cikin jiga-jigan wanda ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Tinubu take bai wa wadanda ba ‘yan siyasa manyan mukamai masu gwabi tare da yin watsi da ‘yan siyasan da suka wahala wajen kafa wannnan gwamnati.
“Ina mai tabbatar da cewa mutane sun damu kwai da gaske. A lokacin yakin neman zabe, mafi yawancin wadanda ke samun manyan mukaman ba su yarda da manufar shugaban kasa ba. Yawancinsu sun yaki manufofin jam’iyyarmu.
“Amma yanzu ana ce mana su kadai ne za su iya rike wasu bangarori masu maiko. Amma babu wani dan siyasan da bai kware a wani bangare ba. Hasali ma, mun kwararru ne a fannoni daban-daban,” in ji shi.
Wasu rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban kasa ta bukaci kungiyoyi daban-daban su mika sunayensu domin samun mukamai a shekarar da ta gabata, sai dai an bayyana cewa da yawan jiga-jigan APC an cire sunayensu.
Wata majiya ta bayyana cewa tuni dai wasu daga cikin jiga-jigan sun hakura ganin yadda gwamnatin ta kusan shafe shekara daya babu wani labari.
“Abun dariya ne a cewa har yanzu mutanenmu suna jiran a fitar da sunayensu, wanda a yanzu an doshi shekara guda. Mafi yawancinmu ana bayyana mana cewa fadar shugaban kasa ba ta manta da duk wadanda suka taimaka mata ba, amma mutanenmu sun fara hakura,” in ji wata majiya.
Wasu da dama suna tunanin cewa za su sami mukami domin kuwa suna da masaniyar cewa sunayensu suna gaban mai girma shugaban kasa, ta hanayar wadanda suke da fada-a-ji musamma ma wadanda suke dasawa da shi a watannin baya.
Bincike ya nuna cewa fadar shugaban kasa na nan na aiki a kan nade-naden mukamai a hukumomin gudanarwa na ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati tare da jakadun kasashe mabambanta.
A shekarar da ta gabata shugaban kasa ya kafa wani kwamiti da suka hada shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin Tarayya, Senator George Akume domin su yi aiki a kan nade-naden mukamai, sai dai har yanzu ba a kara jin wani abu ba daga wannan batu.
Wata majiya da ke kusa da gwamnati, ta bayyana cewa batun rahoton Oron-Saye ya kawo tsaiko game da nade-naden mukmai wanda har yanzu ba a kammala ba.
“Gwamnati tana yin nazari a kan yadda za ta aiwatar da rahoton Orosaye domin duba mai yiwuwa a nade-naden mukamai ga mutane a ma’aikatu da aka hadesu ko kuma aka rage su. Wannan shi ne makasudin da ya sa aka samu tsaiko,” in ji wata majiya daga gwamnati.
Haka kuma nade-naden da aka yin a shugabannin gudanarwa a jami’o’in gwamnatin tarayya ya haifar da wasu matsaloli hukumomin gudanarwa na wasu jami’o’I da dama.