Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa ma’aikatan ?asar al?awarin cewa nan gaba ka?an gwamnatinsa za ta ?ara musu albashi, kamar yadda ya bayyana cikin jawabinsa a yammacin Litinin.
Kazalika ya sake cin alwashin ?ullo da matakan sau?a?a wa ‘yan ?asa ra?a?in da suke ji na cire tallafin man fetur, wanda ya ce “wasu mazambata ne ke amfana da shi”.
“A cikin wata biyu, mun adana sama da naira tiriliyan ?aya na tallafin mai da ake kashewa kan abin da babu riba kuma ‘yan sumoga da mazambata ke amfana,” kamar yadda ya bayyana.
Cikin jawabin da ya gabatar na minti 20 ta kafar talabijin ?in gwamnatin ?asar, Tinubu ya nemi ‘yan Najeriya su ?ara ha?uri.
Cikin matakan da gwamnatin ta Tinubu ?auka, akwai ba da umarnin rarraba tan 200,000 na hatsi a fa?in ?asar don a sayar kan “sassau?an farashi”.
Sai dai jawabin shugaban bai ta?o batun soke tsauraran sharu??a ba game da dokar bayar da bashin ku?in karatu, wanda gwamnatinsa ta ba da sanarwa jim ka?an kafin ya fara jawabin.
Ga wasu al?awura biyar da shugaban ya yi wa ‘yan ?asar.
‘Za mu ?ara muku albashi’
Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na dab da ?ara wa ma’aikatan Najeriya albashi.
“?arin albashi na nan tafe,” a cewarsa. “Da zarar mun daddale game da mafi ?arancin albashi da kuma sauran abubuwa, za mu saka shi cikin kasafin ku?i domin fara aiki da shi cikin gaggawa.
“Tuni mun ?addamar da tsarin sake duba albashin ma’aikata.”
Bai wa kamfanoni 75 rancen biliyan 75
Bugu da ?ari, shugaban ya ce manufarsu ita ce samar da aikin yi ta hanyar bai wa kamfanoni 75 rancen ku?i naira biliyan 75 cikin wata tara masu zuwa.
“Don ?arfafa ?angaren samar da kayayyaki da kuma ayyukan yi, za mu kashe naira biliyan 75 daga Yulin 2023 zuwa Maris na 2024. Tunaninmu shi ne bai wa kamfanoni 75 damar ha?aka tattalin arziki.
“Kowane kamfani daga cikin 75 ?in zai iya samun rancen biliyan ?aya kan kashi 9 cikin 100 na ku?in ruwa duk shekara, inda za su biya cikin shekara biyu a matsayin shiri na dogon lokaci, da kuma wata 12 na fara aiki.”
Baya ga wa?annan, Tinubu ya ce za su bai wa masu ?ananan sana’o’i tallafin biliyan 50, inda mutum 1,300 za su amfana a ?ananan hukumomi 774 na fa?in Najeriya.
Raba tan 200,000 na hatsi, taki
Haka nan, Shugaba Tinubu ya ce daga cikin matakan da suka ?auka na rage ra?a?in akwai rarraba hatsi ga iyalai da kuma taki ga manoma a fa?in ?asa.
“Za mu tabbatar da cewa akwai abincin da aka saba ci kuma cikin sau?i,” a cewarsa.
“Wannan dalilin ya sa na ba da umarnin fitar da tan 200,000 na hatsi daga rumubun gwamnati don raba wa iyalai a jihohi 36 har da Abuja a farashi mai rahusa.
“Kuma mun ba da umarnin raba tan 200,000 na taki da iri da sauran kayayyaki ga manoman da ke tallafa wa shirinmu na samar da isasshen abinci.”
Samar da motocin bas masu amfani da gas
Yayin da ‘yan ?asa ke ci gaba da kokawa kan tsadar man fetur, Tinubu ya ce ?aya daga cikin shirinsu shi ne samar da motocin bas masu amfani da makamashin gas (CNG).
“Daga cikin shirinmu, za mu fito da motocin bas a fa?in johohi da ?ananan hukumomi don ?aukar fasinja a farashi mai sau?i.
“Mun samar da hanyoyin kashe naira biliyan 100 daga yanzu zuwa watan Maris na 2024 don kawo rukuni 3,000 na motocin da ke amfani da gas (CNG).”
Noma kadada 400,000 ta shinkafa, masara, alkama, rogo
Har wa yau game da noma, shugaban ?asar ya ce gwamnatinsa za ta kashe naira biliyan 200 cikin 500 da majalisa ta amince masa wajen ha?aka noman shinkafa da masara da alkama da rogo.
“Za mu kashe biliyan 50 wajen noma kadada 150,000 ta shinkafa da masara kowannensu.
“Sannan kuma, mu kashe biliyan 50 wajen noma kadada 100,000 ta alkama da rogo kowannensu.”