Jawabin Shugaban Kasa Na Sabuwar Shekarar 2021

“Bar kan ku ‘Yan Uwana ‘Yan Najeriya Maza da Mata,

Da farko, zan so nagode da dabbaka sunan Allah Mai Girma wanda ya sa muka ga shekarar 2020 da ba mu damar shaida fara wata sabuwar Shekara. Muna godiya ta musamman ga Allah kasancewa shekara ta 2020 ta kasance mawuyaciya tun bayan kasancewar Nijeriya a matsayin kasa.

  1. Zan iya fadin haka kan sauran daukacin kasashen Duniya, sakamakon kalubalen da al’ummar mu suka shiga saboda sabuwar annobar cutar corona.
  2. Yayin kuma da aka aminta cewa 2020 ta kasance shekara mawuyaciya, mun dauki wannan shakarar a matsayin ta tsira da samun damar fita daga cikin mawuyacin hali dama kuma bada sake sabunta fatar cewa zamu sake zamo gwarzayen gurin shimfida mai kyau a Cikin shekarar 2021 dama bayan ta.
  3. A dai-dai wannan lokaci da muka samu damar yin bukin na wannan Shekara ta 2021, dole mu lazimci ‘yan uwan mu Maza da Mata da suka rasu wadan da basu samu ikon ganin wannan shekarar ba. Allah yaji kansu da rahma.
  4. Dole mu tuna da cewa munyi biki mai cike da Tarihi na samun ‘yancin kan kasa shekaru Sittin a matsayin kasa mai iko ranar Daya ga Watan Oktoba 2020. Cikin fata mai kyau da Godiya, zanso na sake tunatar damu cewa a matsayin kasa da muka fuskanci kalubale a yayin zamo kasa kuma Babba mai Daraja, mun kunyatar da masu sukar mu na ciki gida da kasashen Duniya wadan da basu taba tsammani zamu dore har izuwa wannan lokacin ba da Duniya zata datake damawa damu dama Dorewar mu tun bayan kasancewar mu kasa shekaru da dama ranar Daya ga watan Oktoba na 1966.
  5. Duk da haka, gashi munkai inda muke, Shekaru Sittin da daya zamu kai a bikin murna dazamuyi watan Oktaba dake tafe nan gaba, ba kawai mun kai nan bane, mun tsaya kyam a matsayin kasa cikin Lumana da hadin kai karkashin Hukuncin Allah sama kuma aiki don son Cigaba da yan Najeriya Wanda yasa muka kai haka, shekara bayan Shekara, tsawon shekaru Gommai, yanayi na dadi da sabanin haka mun fito da karfin dama kyau a inda wasu suka gaza dama rududdugewa. Wannan kasa, wannan Najeriya zata tsira dakuma Bunkasa.
  6. A wannan tafiya tamu amatsayin kasa, mun samu ganin Cigaba da koma baya, Shekarar 2020 hakika yazo da kalubale da dama, wanda yasamo asali daga Tsaro da batun da yashafi Tattalin Arziki a daukacin yankunan mu da zanga zangar da muka fahimci cewa ya samu jagorancin Matasan mu wanda yazamo kamar ankarar wa ne kan bukatar yin sauye sauyen a aikin Jami’an ‘yan sanda da tabbatar da aiki bisa Doka. Gwamnati taji, wannan Gwamnati ta saurara kuma wannan Gwamnati a shirye take ta cika Alkawura Biyar data na Bukatun Matasan, kwarai mun fahimchi cewa dukkan mu fata muke mai kyau ga kasar mu Najeriya.
  7. A tsakiyar wadan nan dumbin kalubale, Tuni nayi Alkawari cewa a matsayina na Zababben Shugaba kuma Babban Kwamandan Askarawa, zan tabbata cewa wadan nan Matsaloli dake nan akwai zamu fuskanceshi gadan gadan da sake sabunta kudurorin mu da dukkan hanyoyin da suka dace na Gaugawa da ake bukata. Munji dukkan korafe korafen ku zamu kuma cigaba da saurarar ku, kuma dukkan masu ruwa da tsaki wadanda suka dukufa domin hadin kan Najeriya don tabbatar da cewa kowani yanki na kasar nan ya zauna lafiya domin mu baki daya, yayin kuma baku tabbacin cewa bada kariya ga makomar masu tasowa nan gaba.
  8. Zan kuma so nayi imfani da wannan lokaci farin ciki sabon Shekara domin sake Jaddada jajircewa ta ga Mutanen Najeriya, Musamman Matasa muna bukatar hadin kanku da goyon baya. Gurin Samar da tsaron kasa da muke bukata domin tabbatar da makoma mai kyau wa Matasa.
  9. Matasan mu masu sune mafiya Daraja a gida ko kasashen ketare. Dabar ba runsu, Kirkire Kirkire, da kawo sabbin da hanyoyin kasuwanci sanannen abune garemu duka. Dayawan Matasan mu sunyi fice a fannoni daban daban da rayuwa wanda yahada da Wasanni, Mishadantar wa, Sadarwa, limin Sadarwa na Zamani, Kasuwanci duk Duniya sun yadda wadannan Nasarori ne.
  10. A matsayin Gwamnati mun dukufa cikin aikin sanya matasan mu cikin harkokin kirkire kirkire ga Mutanen mu. A kan wannan batu, zamuyi aiki kafada da kafada da Bangaren Majalisa domin samar da yanayin mai kyau dazai bada dama maida hankalin mu kan dabarun da zamu mara baya, dazai mazo a kowani yanki. Wannan zai samar da dama mai dunbin yawa a bangaren fasaha da nishadantar wa.
  11. Shekarar 2021 shakka babu zai zamo muyi aiki domin karfafa kyakkyawar fatan ga ‘Yan uwa ‘yan Najeriya a mahangar Kasa mai hadin kai da Cigaba. Wannan Gwamnati zata cigaba da maida hanakali domin Samar da bada fifiko ga manyan tsare tsare karkashin shiri abinda aka sa gaba na “SEA” Security, Economy and Anti-Corruption) Agenda. Wasu daga cikin wurare daza’a basu fifiko kai tsaye zamu maida hankalin mu da karfafa su wanda ya kunshi:

A KAN TSARO:

  1. Kara kaimi da sake fasali manyan Jami’an tsaro da Jami’n Soji da ‘yan Sanda da hangen kara karfafa hanyoyin gudanar da aiki da sanya da rarrabe yadda aiki jami’an tsaro zai gudana kan masu kishin gani kasheni da Gungun miyagu na gida da kasashen ketare dasuke yakar Al’ummar mu a wasu Sassan kasa.
  2. A dangane da kalubalen tsaro da muke fiskanta, a matsayin kasa, zanso na kara jaddada alkawarin da nayi kwanan nan a sa’ilin da aka sace yaran mu sama da Dari Uku 300 a Makarantar Sakandaren kimiyyar Gwamnati dake Kankara, wadan da cikin Nasara Jami’n tsaron mu suka ceto su.
  3. Kwarewa da Jami’an tsaron mu suka nuna, da hadin gwiwa daga Masu Fada aji da suka fito daga jihohi da Gwamnatin Tarayya Wanda yayi sanadin Samun Nasarar Ceto Yaran shaida ce cewa kasar Najeriya akwai tsaron cikin gida daza iya magance hare haren ‘yan Ta’dda akan ‘Yan kasar mu.
  4. Duk da haka, mun fahimci cewa dole a cikin gaugawa sake zage Damtse don shiga tsakani halin da ake ciki domin tabbatar da wadan nan munanan abinda ke faruwa bai zamo jiki ba. Gwamnatin mu tana cike da masaniyar hakkokin dake rataye a wuyar ta na kare rayuka da Dukiyar dukkan ‘yan Najeriya, kuma baza muyi sako sako ba gurin kara fahimtar da daukan darasi akan sabbin Barazana ga tsaron kasa da wanzuwar mu ba.

A KAN TATTALIN ARZIKI:

  1. Hankalin mu yanaga sake Inganta Tattalin Arzikin mu ta hanyar shirin Sauya fasalin Tattalin Arzikin kasa wanda zai Mara baya ga matakin farko na Samar da wadataccen abinci da kan mu. Wannan ya taimaka gurin rage yawaitar hawa hawan jadawalin kayan masarufi da yin la’akari da matakin mai kyau gurin samar da abinci a lokacin kulle na Annoba.
  2. Yanzu haka muna kuma sake gina muhimman aiyuka dake a kasar da cigaba, da gabatar da Sauyi ta hanyar aiwatar da Gyare Gyare, Sake Fasaltar da Fadada tsarin Jiragen Kasa, Hanyoyin kasar mu da Gadoji dake a Birane da Kauyuka, dama Tashoshin Jiragen sama dana Ruwa.
  3. Gyare Gyaren da muka aiwatar dasu a bangaren Lantarki zai samar da tabbacin karuwar wadataccen lantarki a kokarin da ganin munyi Nasarar fadada Samar da Rarraba Wutan Lantarki don imfani dashi a cikin gidaje da Kamfanoni.
  4. A matsayin Gwamnati yanzu haka muna sake tsara wasu sabbin aiyukan dazai kara karfafa samar da Guraben aiki da mara baya ga hanyoyin kasauwanci ga Matasan mu.
  5. Tare da bude iyakokin kasar cikin kwanakin nan da suka gabata, muna sa ran cewa za’a kara sanya bukatar bin ka’idojin ketare iyakar kasar da yarjejeniyar kasuwanci na kasa da kasa zai kara karfafa fata mai kyau da muke da ita ga dayawan kananan kasuwanci da harkokin Noma masana’antu da kasuwanci da kasar ta dogara dashi.
  6. Sako da muke dashi ga Kasashe makwabta na yankin Afirka ta Yamma shine, Najeriya ta bude iyakokin ta ne ga wadan da keda niyar yin kasuwanci ta hanyoyin da doka ta tsara.

A KAN YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA:

  1. A kan yaki da cin hanci da raahawa wanda yana daga cikin jagororin Gwamnatin mu, Mun samu Nasarori Manya kawo Yanzu kuma a wannan Shekara, mun sake zage Damtse domin cigaba a tafarki ganin mun kauda Cin hanci da Rashawa, ta hanyar aiki kafada da kafada da dukkan Madafun Gwamnati domin samun nasarar aiwatar da wannan fada da muke da rashawa da cin hanci.
  2. Yayin dazamuyi aiki tareda bangaren Majalisa domin Samar da Dokoki dazai karfafa yaki da Cin hanci, zamu kuma zamo masu kara ganin sake dubi kan wasu cikin dokoki ta yadda zasu tabbatar cewa wannan yaki ya samu nasara. A bangaren mu na Zartaswa, zamu tabbatar da yin aiki cikin nutsuwa da yanke hukuncin Shara’a Cin Hanci da rashawa akan lokaci, yayin da muke rokon Bangaren Shara’a da su tabbatar cewa Shara’oin Cin Hanci an yanke hukunci su kan lokaci daya dace.
  3. Kan cigaba da samun karuwar nau’e nau’en tashin hankali daban daban dayake faruwa a wasu Sassan kasa, rashin fahimta dake tsakanin kabilu wanda yasamu asali tun shekarun baya ana kokarin ganin ansamu Amintaka, da Mutuntawa da Zama lafiya ana masa marazana.
  4. Koaubalen Rashin Tsaro kai tsaye ya janyo rashin daidaituwar Harkokin Tattalin Arziki, Habaka da Cigaba, inda yake maida mu baya a muhimman gurarare ta hanyar lalata kayaki Gwamnati da Kamafanonin sanya jari.
  5. A wasu Sassan Kasa inda Katutun Talauci, Rashin ababen more rayuwa da bakin cikin rashin Samun abinda yadace ga wasu bangaren Matasa tuni hakan yariga yazamo matsala, yawaitar rikici da kungiyoyi marasa imani irin su Boko Haram suke aiwatar wa da wasu ya zaburar da Gwamnati don daukar manufofi don saukakawa da sanya jari dazai samar da sauyi mai kyau akan rayuwar ‘yan kasa.
  6. Ina sane da cewa wasu cikin nasararorin da muka chimma tun bayan hawa karagar mulkin wannan Gwamnati baiyi kusa da ko da abinda wa ‘yan kasarmu sukaso mu cimma ba. Bazan rike wasu abu dasu so akan fata, da suke mai kyau da suke dashi ga kasar
  7. Duk da haka, Ina kiraga dukkanin ‘yan Najeriya da suyi tunani cikin nutsuwa yanayin da muke kafin hawa karagar mulki, su duba kan gaskiyar abinda kenan mukayi da dan abinda muke samu tun shekarar 2015.
  8. A matsayin mu na Mutane, mun nuna kyauta tawa a dukkan halin da muka tsinchi kai ciki, mun dai daita al’amura da dama cikin gaugawa da aka samu koma baya akan su,
  9. Wadan nan halayya ya karfafa Najeriya cewa “Zata iya, zata yi” wanda wannan ya kara bani karfin fata mai kyau cewa zamu iya kaiwa ga inda muka nufa da cika kiran hadin kai, musamman da karfafan kudurori da muka sanya a sabon Shekara.
  10. Sanya kasar mu cikin aiyukan cigaba aikine wanda dukka ya ke ke kammu. Akan wannan, Sanya lafiyar kasar mu daga Cutar Korona a dai dai lokacin da wannan Gwamnati ta kammala shirin sayo wadataccen Allurar Rigakafin Korona domin rarrabashi, Ina bukatar dukkan ‘yan uwana ‘yan kasa dasu kiyaye Matakan kariya na Cutar Korona.
  11. A matsayi na na Zababben Shugaba, Alkawari na gareku iri daya ne kamar sauran lokuta; zanyi nawa bakin kokari ba tareda da tsoro ko son kai ba. Ina gayyatar dukkanin mu muyi iri guda. Shine hakkin dake wuyar mu na wadan da suka Samar da kasa. Abune da muka son cimma ga abinda kasa ta bada fifiko akai ga bukatun kowa.
  12. Allah ya ja kwanan ‘Yan Najeriya da Ruhin zama Daya da Hadin Tarayya da Hadin kai.
    Allah ya Albarkaci Gwamatin Tarayyar Najeriya.
    Ina muku fatan Sabon Shekara mai Yalwa.

Allah ya Albarkacin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Related posts

Leave a Comment