Jarrabawar WAEC: Gwamnati Ta Yi Amai Ta Lashe

A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewar zata gana da gwamnonin jihohi akan yiwuwar bude makarantu musamman dan rubuta jarabawar kammala sakandire WAEC da aka shirya farawa a ranar 5 ga watan gobe.

Ministan ilimi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa a fadar shugaban kasa inda ya shaidawa manema labarai ciki har da wakilin jaridar muryar ‘yanci a fadar shugaban kasa, inda yace ”bayan dogon nazarin da mu kayi da kuma la’akari da yawan karuwar masu dauke da cutar korona a fadin kasar nan wanda alkaluman a halin yanzu ya kusa kai dubu 30. Dan haka ya zama wajibi mu kare daliban mu daga fadawa cikin halakar cutar covid 19.

” Dan haka daliban Najeriya da zasu rubuta jarabawar kammala makarantar sakandire (WAEC) ba zasu zana jarabawar a wannnan shekarar ba. Mun gummace daliban mu su rasa jarabawa Waec da su fada cikin halaka.

Labarai Makamanta

Leave a Reply