Wasu lauyoyi sun kafa sabuwar kungiyar lauyoyin Najeriya da manufar kare hakkin su wanda sashi na 40 na kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Ana ganin wannnan mataki da suka dauka bai rasa nasaba da janye gayyatar da NBA taiwa gwamnan jihar Kaduna wanda ya janyo korafi ta ko ina.
A wata takarda da Batista Nuhu Ibrahim Esq da Abdulbasit Suleiman Esq suka saka hannu kuma suka mika ga manema labarai, sun ce lamarin ya matukar taba duk wani lauya ballantana na yankin arewacin kasar nan.
“Abinda ke faruwa a cikin kwanakin nan ya bayyana gazawar kungiyar lauyoyin Najeriya na yadda bata iya hada kan jama’a masu banbanci da ke karkashin kungiyar tare da kare dukkan hakkokinsu.
A matsayin kungiyar wacce ta samu horarwa wurin tabbatar da ci gaba tare da kare hakkin jama’a da ‘yancinsu, ya kamata NBA ta kafu fiye da duban yanki ko kabilanci. “A don haka, ba za mu zuba ido mu ga kungiyar lauyoyin tana kin kare hakkin mambobinta tare da ‘yancinsu. Ya kamata a ganta tana aikata abinda take kira a kan shi.
” Ya bayyana cewa, ‘yan sabuwar kungiyar lauyoyin tuni suka fara tuntubar manyan lauyoyin arewacin Najeriya domin saka ranar da za a rantsar da sabuwar kungiyar.