Tsohon Sarkin Kano Sanusi na II ya ce bai ji dadin takaddamar da ake ba tsakanin kungiyar lauyoyin Najeriya da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai musamman kan matakin da NBA ta ɗauka na janye gayyatar da ta yi wa gwamnan ta halartar taronta.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne lokacin ziyarar da ya kai wa gwamna inda ya ce ce ziyarar ta zumunci ce zuwa ga abokinsa wacce ba ta da wata nasaba da takaddamar da gwamnan yake yi da NBA.
Ziyarar tsohon Sarkin a Kaduna wacce ita ce ta farko da ya kai a wata jiha a Najeriya tun bayan cire shi daga gadon sarautar Kano, ta ja hankalin ƴan Najeriya musamman a shafukan intanet musamman a lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan janye goron gayyatar da ƙungiyar lauyoyin Najeriya ta yi wa gwamnan.
Tsohon Sarkin wanda ya ce gwamna El-Rufa’i amininsa ne ya kuma ce ziyayar da ya kai masa ta zumunci ce da nuna godiya da tsayawa bisa ƙaunar da ya nuna masa kuma ba ta da nasaba da NBA.
Yadda zargin keta haƙƙin dan adam da kasa magance kashe-kashe a kudancin Kaduna da ƙungiyar lauyoyin ta yi wa El-Rufa’i ya ja hankalin ƴan Najeriya haka ma ziyarar da tsohon Sarkin Kano ya kai wa gwamnan na Kaduna.
A bidiyon da gwamna El-Rufa’i ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon Sarkin na Kano ya ce bai ji dadin takaddamar ba musamman matakin da NBA ta ɗauka na janye gayyatar da ta yi wa gwamna El Rufa’i.
“Na karanta zargin da suke, ina ta neman takaimaiman zargin da suke. Idan kun ce wani ba ya mutunta doka, to ta yaya yake ƙin mutunta dokar? Idan kuka ce wani ya kasa magance rikici, ta wace hanya?”
Sarkin ya ce yana fatan wannan takaddamar ba za ta rikiɗe ba ta koma ta addini ko ƙabilanci.
Tsohon Sarkin ya ce kamata ya yi ma Ƙungiyar lauyoyin ta bari sai ya halarci taronta ta yi masa wannan ƙorafin da inda take ganin ya gaza da waɗanda suka dace kuma don ya kare kansa.
Ya ce Ƙungiyar Lauyoyin ta yi hasara, domin halartar gwamnan zai ƙara ƙayatar da taronta kuma za su ƙaru sosai da fahimtar aikin da yake yi.