Da misalin karfe 7:30 na yammacin Talata, Jam’ian tsaro suka dira gidan shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, inda suka gudanar da bincike.
Daya daga cikin masu gadin gidan ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an tsaron sun dira gidan Magu dake Maitama da kuma gidan sa na kan sa dake Karu.
Ya kara da cewa bayan sun gama binciken gidan, sako sako, daki dai, kurdi-kurdi sai suka fito suka ba da takarda muka sa hannu.
” Ba su tafi da komai ba.”
Fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu. Wannan sanarwa bai bayyana ga manema labarai ba sai dai majiya daga fadar shugaban kasa da hukumar EFCC sun tabbatar wa mana cewa an dakatar da Magu daga cigaba da shugabantar hukumar EFCC.
Idan ba a manta ba Magu ya kwana tsare a hannun jami’an tsaro masu binciken musamman.
Majiya ta tabbatar da cewa bayan an shafe tsawon lokaci ana yi masa tambayoyi, an bada umarnin a tsare shi a hannun Ofishin ‘Yan Sandan CID da ke Area 10, kusa Hedikwatar Sojojin Sama, na Kasa da na Ruwa.
Majiya daga iyalin sa sun tabbatar da cewa bai kwana a gida ba. Haka ma majiya a cikin EFCC ta ce bayan an yi masa tambayoyi daga bakin Kwamitin Bincike, sun bada shawarar a tsare shi a hannun ‘yan sanda.
Magu, wanda ke da mukamin Kwamishinan ‘Yan Sanda, majiya ta ce yayin da wasu ke ba da shawarar a tura shi kotu, wasu kuma a cikin ‘yan kwamitin na ganin cewa a nemar masa mafita mai sauki, wato a sauke shi salum-alum.