Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa Jami’an tsaro tare da taimakon yan Bijilanti sun samu nasarar ?akile mummunan nufin kai hari na yan ta’adda a garin Magami, ?aramar hukumar Gusau, jihar Zamfara.
An ruwaito cewa yan bindigan a kan dandazon Babura sun yi yunkurin shiga garin da yammacin Lahadin nan, amma jami’an tsaro suka fatattake su.
Wani Mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Babangida, yace mutane ba su yi wata-wata ba wajen sanar da jami’an tsaro, yayin da suka ji labarin zuwan yan ta’addan.
“Mutane sun koma gefe, wasu sun fara gudun neman tsira. Yan kasuwa sun gar?ame shagunan su, sun koma gidajen su domin shirya wa da jiran ko ta kwana.” “Sun zo a Babura da yawan gaske, suka taru a kusa da Sabon Garin Dutsen Kura, wanda ke nisan kilomita 15 daga garin Magami.”
“Yayin da mazauna suka ji burbushin abin da ke shirin aukuwa, sai suka yi gaggawar sanar da jami’an tsaron dake zaune a garin Magami.”
Bayan samun bayani, jami’an tsaro da kuma yan Bijilanti, sun shirya kan su a bayan gari, suka jira isowar yan ta’addan. “Jami’an tsaro da Yan Bijilanti sun shirya kan su a filin Sallar Idi dake gabashin garin kuma bayan haka ba da jimawa ba yan ta’adda suka ?ariso.”
“Sun yi gumurzu tsakanins su, amma bisa tilas yan bindigan suka gudu, sai da suka rabu biyu saannan kowane ?angare ya yi takansa.” Tun a baya dai, yan ta’addan sun yi yunkuri lokuta daban-daban na kai hari garin Magami amma har yanzun Allah bai ba su nasara ba.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunar yan anda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ci tura.