Kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kaduna da takwarar ta ?ungiyar Kiristoci CAN ta Jihar sun yaba gami da Jinjinawa kokarin gamayyar kungiyoyin Mata masu ya?i da cutar Covid 19 a fa?in Jihar Kaduna.
Babban Sakataren ?ungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Kaduna Malam Ibrahim Kufena ya yi wannan yabon a madadin ?ungiyar, lokacin da tawagar matan suka ziyarci ofishin ?ungiyar dake Kaduna.
Ibrahim Kufena ya bayyana cewar ?ungiyar ta Jama’atu na da rassa na kananan hukumomi guda 23 a fa?in Jihar, kuma babban abin da suka sanya a gaba shine ilimantarwa gami da wayar da kan jama’a akan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar.
Bisa ga haka ?ungiyar ta Jama’atu ta yaba ?o?arin kungiyar matan akan namijin ?o?arin da suke yi na wayar da kan jama’a, tare da yin alkawarin bayar da dukkanin goyon bayan da ya kamata domin samun nasara.
Shima anashi bangaren Shugaban ?ungiyar Kiristoci ta ?asa reshen Jihar Kaduna CAN Joseph Hayab ta bakin Sakataren riko na kungiyar Caleb Maaji, ya tabbatar da bada goyon bayan ?ungiyar CAN akan ayyukan Matan wanda ya bayyana da cewar aikin Allah ne.
Sakataren na CAN ya kara da cewar yana da tabbaci da kwarin gwiwa akan Allah zai taimake su akan aikin jin kai da suke, kuma suna addu’a a kusan kullum da rokon Ubangiji ya kawo karshen wannan cuta.
Tun farko da take gabatar da jawabi Jagorar ?ungiyar Matan Dr. Lydia Umar ta bayyana cewar, babban kudirin da kungiyar tasu ta sanya a gaba shine taimakon gwamnatin jihar Kaduna wajen ?ara wayar da kan jama’a dangane da yadda za su kare kansu daga cutar.
Ta kara da cewar gamayyar kungiyoyin suna da Mata akalla 30 wadanda dukkanninsu suna jagorantar kungiyoyi daban daban wadanda aka samar domin wayar da kan jama’a da yaki da wannan cuta ta Covid 19.