Jama’ar Borno Na Kawo Cikas Wajen Samar Da Tsaro – Rundunar Soji

A ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu ‘yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami’an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike da gano ‘yan ta’adda.

Kakakin rundunar sojin, manjo janar John Enenche, ya bayyana a gidan talabijin na Channels inda yace abubuwan da ke kawo tabarbarewar tsaro har da yadda mazauna yankuna suke kin bayar da bayanai wadanda za su taimaki sojoji.

“Wannan shine damuwarmu. Yana matukar damun mu, muna bukatar bayanai, su ne mazauna yankunan, idan sun ga wata matsala ta barke, yakamata su sanar da mu,”.

Ya ce idan sun tafi sintiri, lokacin da zasu dawo sai suga wasu abubuwan da basu amince da su ba a hanyoyi, kuma mutanen yankunan suna sane da ‘yan ta’addan, amma sai su ki fadi musu. Wannan ita ce babbar matsalar da suke fuskanta.
“Kuma ba zai yuwu mu matsa musu don su sanar damu matsalar ba.” A cewarsa, sojoji ne suka raka gwamna Zulum zuwa inda aka kashe mutane 43 din.

Sannan yace yaji labarin Majalisar ɗinkin Duniya tana cewa mutane 110 ne aka kashe, amma su dai sojoji sun kirga gawawwaki 43 tare da mazauna kauyen, kuma a kan haka za su zauna.
Amma za su cigaba da bincike don tabbatar da asalin yawan mutanen.

Labarai Makamanta

Leave a Reply