Jakadan Najeriya a kasar Jordan, Alhaji Haruna Ungogo ya rasu a ranar Lahadi da ta gabata, ya rasu ne bayan jinyar da yayi ta kwana biyar a babban Asibitin Garki da ke birnin tarayya Abuja.
Majiya daga iyalinsa ta ce za a yi jana’izarsa a a yau Litinin a gidansa dake birnin Kano.
Ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa.
Kafin rasuwar tashi yayi aiki da gwamnatin jihar Kano a matsayin sakataren gwamnati, daga baya kuma ya zama Shugaban Kwalejin Kimiyya da fasaha da ke jihar Kano.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaɓeshi a matsayin Jakada a shekarar 2016.
Allah muke roko ya jiƙanshi ya gafarta mishi Allahumma Amin!