Jahilci Ya Taimaka Wajen Tabarbarewar Tsaro A Najeriya – Me LA

Tsohon ‘dan takarar kujerar majalisar dattawa a shiyyar mazabar Kaduna ta tsakiya, Hon Lawal Adamu Usman Mr LA ya bayyana rashin ilimi a matsayin babban abinda ke kawo wa kasarmu koma baya musamman a fannin Tsaro.

Mr LA ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin ganawa da manema labarai a shirye shiryensa na biyawa daliban jami’a kudin makarantar wannan shekara sakamakon karin kudin da gwamnatin Jihar Kaduna tayi, Mr LA ya kara jaddada aniyarsa na tallafawa daliban jihar Kaduna da kudaden makaranta har sai inda karfin sa ya kare. Mr LA yace ” wannan tallafi da muke bayarwa muna yinsa ne don kowa ya anfana bawai dole sai Wanda ke mazabar Kaduna central ba, kowa zai iya samu domin ba musan Wanda zai taimaki matasan mu nan gaba ba a cikin yaran da muke tallafawa.

Muna kokarin ganin an fadada Shirin yadda kowa zai anfana Nan gaba Kuma muna kara Jan kunnen mutanen Kaduna akan su tabbatar da suna zabe domin chanchanta domin idan suna zaben mutane irinsu Elrufai a Nan gaba Babu abinda zasuyi sai Dana sani” inji Mr LA

Labarai Makamanta

Leave a Reply