Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bayyana ce duk matsalolin da mu ke ci a halin yanzu a kasar nan, babban abinda ya haddasa shi rashin ilimi ne, watau bakin Jahilci da farin jahilci, wanda ya ke kawo matsalar ‘yan bindiga da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi da yin biris din hukumomi ga matasa shi ne musababbin matsalolin da kasar nan ta samu kanta.
Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka a karamar hukumar Kaita, a lokacin da ya ke hannanta gidan marayun da makarantar islamiyya da Sanata Abubukar Sadiq Yar’adua, ga kungiyar Izala ta kasa, karkashin jagorancin Shugabanta Sheikh Abdullahi Bala Lau, domin ci gaba da gudanar da ita.
Masari ya ci gaba da cewa wadannan yara da muke watsarwa, mu ke gani ba ‘yayan mu ba ne, duk halin da za su shiga bai shafe mu ba, ba haka bane. Wadannan yara su za so hana namu jin dadin. Nijeriya ba matsiyaciyar kasa ba ce, abinda ya rage yara su tashi tsaye da neman ilimi na boko da na addinin musulunci, saboda kowacce irin sana’a ce tana bukatar ilimi, ka zamanto kana da ilimi ko da mafi kankanta shaida ce, wadda za ta inganta rayuwar ka, arziki Kuma na Allah ne. Amma ya kamata mu shirya al’ummar mu, Malamai akwai aiki gaban mu.
Daga karshe, Gwamna Aminu Bello Masari ya hannanta takardun gida da islamiyya da kuma wani katafaren fili dake cikin garin Katsina ga Shugaban kungiyar JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, domin cigaba da tafiyar da su.