Iyalan Mai Tallan Jarida Na Neman Diyyar Miliyan 500 Ga Kakakin Majalisa

Iyalan Marigayi Ifeanyi Okereke, wani mai sayar da jarida da mai tsaron lafiyar Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya bindige har lahira sun bukaci naira miliyan 500 daga gare shi a matsayin diyya.

A makon da ya gabata ne wani jami’in hukumar tsaron farin kaya (DSS) Abdullahi Hassan da ke tsaron shugaban majalisar, ya harbe Okereke, a yayin da yake gudanar da sana’arshi ta sayar da Jarida a birnin tarayya Abuja.

An ruwaito cewa bukatar neman biyan diyyar na kunshe ne a cikin wata takarda da lauyan iyalan Marigayin Mike Ozekhome ya aikewa Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila.

A wasikar mai dauke da kwanan wata 23 ga Nuwamba, iyalan Okereke sun ce abin da suka nema ba zai iya maye gurbin dansu ba. “Wanda muke karewa sun umarci da mu nemar musu wadannan hakkoki daga wajen ku:
Kayi amfani da matsayin ka wajen ganin an gurfanar da jami’in tsaron ka (Abdullahi Hassan), wanda saboda jin dadi, ya fita daga hurumin aikin sa ya kuma harbe mutumin da bai ji ba bai gani ba,” a cewar Ozekhome.

“Kuma ka biya iyalan Okereke Naira miliyan 500 kacal. “Biyan wannan kudi baza su iya maye gurbin sa a matsayin ɗa, miji, da kuma dan uwa ba. Amma hakan zai rage bakin ciki da kuma radadin da kunchin rayuwa da mutuwar ta sa su.”

Kuma lauyan ya bayyana idan aka gaza biyan bukatun cikin sati guda, za su dauki mataki na shari’a. “A kuma lura cewa wannan bukatun wadda muke karewa ne, idan aka ki bi ko a banzatar da bukatar cikin mako guda daga kwanan watan da ke jikin wasikar, zamu dauki matakin da ya dace na shari’a, don bi wa wanda muke karewa hakki”, a cewar sa.

Gbajabiamila ya ce ya mika jami’in gaban rundunar DSS don hukunta shi. Ya kuma ziyarci iyalan don yi musu ta’aziyya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply