Rahoton dake shigo mana daga yankin Gabas ta Tsakiya na bayyana cewa Amurka ta kai tallafin abinci na farko ga al’ummar Gaza ta jiragen sama.
Fiye da kulli 30,000 na abinci jiragen saman Amurka uku suka jefa wa al’ummar Gaza.
An gudanar da aikin rabon abincin tare da hadin gwiwar sojojin saman Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka suka bayyana.
Jami’an Amurka sun ce abincin da aka rabar shi ne na farko daga cikin da yawa da shugaba Biden ya bayyana ranar Juma’a.
Shugaba Biden ya alkawarta kai agajin abinci zuwa Gaza, bayan da aka kashe sama da mutum 100 da ke dakon jiran agajin abincin tallfi ranar Alhamis
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce jiragen saman sun jega kullin abinci 38,000 a wani wuri a Zirin Gaza
A baya wasu kasashe irin su Birtaniya da Faransa da Masar da Jordan sun taba jefa wa al’ummar Gaza tallafin abinci ta sama, to sai dai wannan shi ne karon farko da Amurka ta yi hakan.