Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce Janar Aguyi Ironsi, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo ne suka kafa tushen rashin tsaro a Nijeriya.
Shugaban majalisar sarakunan Nijeriya ya ce dokar Ironsi ta 1966, Gowon ta 1967 da Obasanjo 1976 ne suka kwacewa sarakuna iko.
Ya tabbatar da cewa Turawan mulkin mallaka suna da hikima a dokokin da suka tsara da kuma ikon da suka baiwa sarakunan gargajiya.
Shugaban majalisar sarakunan kasar nan kuma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Alahmis yace mulkin janar Aguiyi Ironsi, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo ne suka bar masarautun gargajiya babu kundun tsarin mulkinsu.
A yayin wani jawabin sarkin a wani taro a Abuja ga kwamitin sake duban tsarin mulkin kasar nan na majalisar, ya ce dokar Ironsi ta 1966, Gowon ta 1967 da Obasanjo 1976 ne suka kwace karfin ikon sarakunan gargajiya suka mika wa kananan hukumomi.
Sarkin Musulmin wanda ya samu wakilcin Etsu Nupe, Alhji Yahaya Abubakar, ya ce wadannan dokokin ne duka samar da rashin tsaro tare da rashawar da kasar nan ke fuskanta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, sarkin ya ce kafin a yi gyaran dokokin kananan hukumomi na 1976, Nijeriya tana samun cigaba, zaman lafiya kuma hade da kyawawan al’adun gargajiya.
Ya yi kira ga majalisar dattawa da su yi kokarin dawo da wadannan karfin ikon na masarautun gargajiya.
Basaraken yace akawai matukar hikima a lamarin Turawa da suka baiwa sarakunan gargajiya tsarin mulki basu bar su kara zube ba.