Iran Ta Damke Shahararriya Jarumar Fina-Finan Kasar

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin ƙasar da ake yi ta shiga wata na huɗu.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ƙarya da kuma ƙokarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta.

Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan.

A makonnin baya, ‘yar fim ɗin ta sanya wani hotonta a shafin sada zumunta babu ɗan-kwali tana kuma rike da allon alamar nuna goyon bayan zanga-zangar da ake yi a kasar.

Tauraruwar ta fito a cikin fim din da ya yi fice mai suna The Salesman.

Labarai Makamanta

Leave a Reply