Ina Taya Sabon Sarki Murna – Yariman Zazzau

Yariman Zazzau ya taya sabon sarki Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murna

Munnir Jafaru yana cikin masu neman sarautar yace ya amince da nadin Bamalli a matsayin ikon Allah.

Ya mika godiya ga magoya bayansa tare da addu’ar Allah SWT ya yi wa sabon sarki jagora a dukkan aiyukansa.

A ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2020 ne Gwamna Nasiru El-Rufai ya amince da nadin Ahmed Bamalli a matsayin sabon sarki don maye gurbin Dr. Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba.

Da ya ke martani kan naɗin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Ya kuma yi addu’ar, “Allah SWT ya yi wa sabon sarki, ya kawo cigaba da zaman lafiya ga al’ummar masarautar.

Ya ce, “Cike da godiya ga Allah SWT, na samu labarin naɗin Magajin Garin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau ga Gwamna Nasir El-Rufai ya yi.

Ya zama dole dukkanmu mu yarda da ikon Allah mu taya sabon sarki Mai Girma Ambasada Nuhu Bamalli murnar nadin da aka masa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply