Ina Neman Mijin Aure – Salmah Umar

Wata matashiyar budurwa mai suna Salmerh Umar ta bayyana a shafin zumunta tana neman mijin aure yayin da ta bukaci ‘yan Nijeriya da su taya ta addu’a, domin burinta ya cika.

Matashiyar budurwar wacce shafinta na Twitter yake a matsayin @SalmerhUmar ta ce ba za ta iya ci gaba da boye yadda take ji a ranta ba.

Salmerh wacce ta kasance ‘yar jihar Gombe, ta wallafa hotunanta guda biyu a shafin nata domin nuna wa mutane irin kyawun da Allah ya yi mata.

Shakka babu matashiyar na so ta dandani zuman da ke cikin aure sannan ta bar duniyar ‘yan matanci.

Wallafar da ta yi ya sa mutane da dama yin sharhi inda suka dunga fadin albarkacin bakunansu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply