Ina Matuƙar Gamsuwa Da Yin Lalata Da Tsofaffi- Matashin Da Ya Yi Wa Tsohuwa Fyade

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Niger ta ce ta kama wani Matashi mai suna Sani Garba mai shekaru 32 a kan yi wa wata dattijuwa mai shekara 60 fyade.

Rundunar ‘yan sandan ta yi gabatarshi a ranar Juma’a ya ce yadda mazaunin tsofaffi ke motsi ne ke jan hankalinsa da tayar masa da sha’awa. Wanda ake zargin ya kuma ce yana jin dadin lalata da mata masu shekaru da yawa a unguwarsu saboda ba shi da kudin neman budurwa.

Ya kara da cewa ya yi wa mata masu shekaru da yawa fiye da uku fyade a unguwarsu, ya ce ya yi nadamar aikata abinda ya kira “shirme”.
“Tunda ba ni da kudin rike budurwa na gwammace in rika lalata da tsofafin mata a unguwar mu kuma ina jin dadin hakan.

“Wasu lokuta na kan tambayi kai na me yasa na ke aikata wannan shirmen?’Na yi takaicin tsintar kaina a wannan halin,” in ji shi.

Wasiu Abiodun,Kakakin rundunar, ya ce jami’an hukumar na ‘B’ Division ne suka kama wanda ake zargin a Suleja da ke jihar. Abiodun ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

An ce wanda ake zargin ya yi kuste gidan wata mata mai yawan shekaru a ranar 18 ga watan Yuli misalin karfe 4:30 na yamma kuma ya yi mata fyade. Hakan na zuwa ne bayan yawaitan fyade da ake samu a sassan Najeriya daban daban.

Labarai Makamanta

Leave a Reply