Ina Mamakin Yadda Wasu ‘Yan Najeriya Ke Neman Ganin Bayan Kasar – Babban Hafsan Sojin Najeriya

IMG 20240308 WA0095

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Christopher Musa ya koka dangane da yadda ake samun kalubale a kokarin da rundunar soji ke yi na magance matsalar tsaro sakamakon yankan baya na wasu marasa kishin ƙasa.

Janar Christopher Musa ya yi wannan furuci ne lokacin da ya ke bayani kan ƙalubalen da ake fuskanta wajen yaƙi da rashin tsaro a tarayyar Nijeriya.

Babban Hafsan Sojin ya kuma koka kan yadda ake samun wasu ɓatagari waɗanda ke yi wa Najeriya yankan baya duk da irin tagomashin da suka samu daga kasar.

Kalaman Christopher Musa na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a ƙasar musamman a yankin arewacin kasar, inda ‘yan bindiga ke aikata abin da suka ga dama, lamarin da ake danganta shi da cewar da akwai goyon baya da suke samu daga wajen wasu jama’a marasa tsoron Allah dake cikin al’umma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply