Ina Jin Dadin Fitowa Muguwa A Fim – Saratu Daso


Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta bayyana cewar, ita fa tana alfahari da rol din da take fito wa na mugunta a cikin fim, domin kuwa tun da ta fara fim da shi aka san ta kuma abi har ya zama jinin jikin ta, don haka babu wani rol da za a ba ta wanda zai yi daidai da ita kamar wannan rol din na mugunta.

Ta bayyana hakanne ya yin da take tattaunawa da wakilin jaridar Dimukaradiyya, inda ta ce “Duk abin da a ke gani wanda na ke yi a fim, ina yin sa ne, domin fadakarwa ga masu hali irin wannan, amma dai ba haka halina ya ke a zahiri ba, domin duk wanda ya sanni a fili ya san ba haka nake ba.”.

Mun tambaye ta ko ita ce take zabar rol na mugunta don haka ta yi suna har aka san ta da shi?

Sai ta ce” A gaskiya ba ni na ke zaba ba, kawai dai labarin ne ya ke kira na kuma ina ganin hakan yana da alaka da tun farkon fara fim Dina da irin wannan na fara, don haka ina fito wa a rol din suruka da zan takura matar Dana, ko kanwar maigida na Hana matan sa jin dadi ko yayar maigida, ko dai na fito a matsayin uwar da na ke takura Dana a kan harkar gidan sa. To duk wannan abin alfahari ne a gare ni, saboda fadakarwa ne ga masu irin wannan halin, kuma Alhamdulillahi, da haka duniya ta sanni, wanda ta dalilin hakan na samu ci gaban rayuwa daga wajen masoya, babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah. ” a cewar ta.

A karshe Saratu Gidado ta yi kira ga abokan sana’ar ta, da su hada kan su, kuma su tsare mutuncin sana’ar da a ke yi.

Related posts

Leave a Comment