Ina Goyon Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Shugaban Matasa

An bayyana cewar ko shakka babu a halin matsalar tsaro da Najeriya ta tsinci kanta a ciki zaman sulhu da ‘yan bindiga shine alheri kuma mafita daga cikin matsalar.

Shugaban kungiyar cigaban matasan yankin Arewacin Najeriya Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa ya bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna.

Kamal Nasiha ya ?ara da cewar kalaman da wasu ke yi na sukar matakin sulhu da ‘yan bindiga kuskure ne babba, domin a tarihin ya?i da sauran fitintinu da Duniya ta yi fama dasu yin sulhu ne ke kawo karshen su ba zubar da jini ba.

Shugaban matasan wanda ya koka dangane da siyasa da wasu ke kokarin cusawa akan harkar tsaro, yace zunubi ne babba caku?a siyasa da harkar tsaro domin lamari ne wanda ba zai haifar da ?a mai ido ba.

Dangane da kalaman da gwamnan jihar Kaduna El Rufa’i ke yi na cewar Kisa ne maganin ‘yan bindiga ba sulhu ba, Kamal Funtuwa yace kalaman El Rufa’i na borin kunya ne domin ?oye gazawarshi.

“Tun kafin wannan matsala ta girma aka ankarar da El Rufa’i da kuma bashi shawarar matakan da ya kamata ya dauka a jihar Kaduna, amma saboda son zuciya ya yi biris da shawarwarin sai a yanzu yake wasu surutai marasa amfani”.

Kamal Nasiha ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya ta da ?auki matakin yin sulhu da ‘yan bindiga domin kawo karshen zubar da jini da satar mutane da ke neman zama ruwan dare a Arewa.

Related posts

Leave a Comment