Ina Fatan Sabuwar Gwamnati Za Ta Dora Daga Inda Na Tsaya A Yaki Da Rashawa – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce cin hanci da rashawa ya kasance babbar barazana da ƙasashe ke ci gaba da fuskanta.

Ya bayyana haka ne jiya a fadarsa da ke Abuja, yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin gudanarwar Kotun Ɗa’ar Ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Yakubu Umar.

Buhari ya ce yana fatan irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ita ma gwamnati mai zuwa za ta ɗora a kan haka.

Ya bayyana Kotun Ɗa’ar Ma’aikata a matsayin muhimmiya ce wajen yaki da rashawa da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya ce irin waɗannan hukumomi suna taimakawa gwamnati wajen yaki da masu satar dukiyar ƙasa.

“Muna fata cewa irin tubali ko kokari da ta yi a ɓangaren yaki da rashawa ya zama mai zuwa ta ɗora kan haka saboda yadda hakan ke barazana ga ƙasashe,” in ji Buhari

Buhari ya kuma gode wa Kotun Ɗa’ar Ma’aikatan saboda irin sadaukarwa da ta yi duk da irin matsin tattalin arziki da kuma raguwar kuɗaɗen shiga da gwamtai ta samu,” inda ya yi alkawarin samar da sabbin tsare-tsare da za su samar da kuɗade ga hukumomin waɗanda ya ce suna da matukar muhimmanci.

Shugaban Kotun, Danladi Umar ya yaba wa gwamnatin Buhari kan irin rawar da ta taka a fannin raya ababen more rayuwa da noma da kuma samar da ayyukan yi da sauransu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply