Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ina Da Tabbacin Tinubu Zai Dora Daga Inda Muka Tsaya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Legas na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya ce ya yi farin ciki da barin tattalin arziƙin Najeriya a hannun ƙwararru. Shugaban mai barin gado ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a wajen ƙaddamar da matatar man Dangote a Legas.

“Wannan babbar masana’anta da muke ƙaddamarwa a yau misali ce ƙarara na abin da za a iya samu idan aka ƙarfafawa ‘yan kasuwa gwiwa da tallafa musu da kuma idan aka samar da yanayin da mutane za su iya saka hannun jari don ci-gaban kasuwanci.”

Buhari ya ƙara da cewa ya na kyautata zaton cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mai jiran gado zai cigaba da yin abubuwan da za su taimaki tattalin arziƙin ƙasa A faɗarsa: “Ina da yaƙinin cewa mutumin da zai gaje ni, mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai ci gaba da inganta tattalin arziƙinmu da kasuwancinmu, tare da bin tsarinmu na ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa don ƙara haɓɓaka tattalin arziƙinmu da bunkasa shi cikin gaggawa.”

“Ina kira da ƙarfafa gwiwar sauran manyan ‘yan kasuwanmu da su yi koyi da wannan fitaccen ɗan kasuwan, su haɗa hannu da gwamnati wajen ƙara haɓɓaka ci gabanmu domin tabbatar da ƙarfin tattalin arzikin da ake kallon ƙasarmu da shi a duniya.”

“Lokacin da na zagaya Afirka kuma na haɗu da ‘yan’uwana shugabannin ƙasashe (kuma naji daɗi wasunsu suna nan wurin), sau da yawa nakan ji a raina cewa ƙasarmu na da albarkatu da jarin ɗan adam domin jagorantar haɓaka tattalin arzikin Afrika, cigaba da kuma cimma burin 2063, na ‘Afrikar da dukanninmu ke so.’”

Exit mobile version