Ministan ya?a labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana nadamarsa guda ?aya da yake ciki a matsayinsa na minista ?ar?ashin mulkin Buhari.
A cewarsa, nadamar tasa bai wuce yadda wasu ?an Najeriya ke ?in yabawa gwamnati duk da irin namijin ?o?arin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke yi da ?an abin da ke a hannunsa.
Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja.
Ya ce duk da ?arancin ku?a?e, babu gwamnatin da ta ta?a kafa tarihin gwamnatin Buhari a gwamnatocin baya a Najeriya.
Musamman wajen ?ir?iro tsare tsare da shirye-shirye da zasu kawar da talauci tsakanin mabu?ata da mata har ma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ministan ya ce nadamarsa ita ce wasu ?an Najeriya sun gaza yaba ?o?arin da gwamnatin ke yi, amma suna murna da abubuwan da ba dai-dai ba.
Babbar nadamata a wannan gwamnatin shine ?an Najeriya sun gaza yabawa abubuwan da gwamnati ke yi da ku?a?e ?alilan.