In Dai Buhari Ya Damu Talaka To Ya Janye Ƙarin Farashin Mai – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta janye matakan da ta dauka a baya-bayan nan na kara farashin man fetur da kuma na wutar lantarki, inda Kwankwaso ya ce za su kara jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

A zantawar sa da BBC Kwankwaso ya ce kamata ya yi gwamnatin ta toshe hanyoyin da kudade ke zurarewa a maimakon karin farashi.

Kwankwaso yace babu hujjar karin kudin man fetur a wannan lokaci Ya ce “Kasashe da yawa a duniya a yanzu shugabanninsu na tausaya musu inda suke fito musu da tsare-tsare ta yadda zasu samu saukin radadin wannan annoba.

Yace amma sai gashi a Najeriya a irin wannan yanayi aka shigo da duka na karin farashin mai da wutar lantarki da dai sauran abubuwa yace A gaskiya da wuya ka samu wani wanda zai goyi bayan wannan tsari’.

Kwankwaso yaci gaba da cewa baya goyon bayan wadannan matakai na gwamnati musamman a lokacin da mutane ke fama da matsaloli iri-iri.

Kwankwaso ya ce idan har gwamnatin Buhari na sauraron jama’arta, to yakamata idan tayi abu ba dai-dai ba to ba abun kunya bane ta gyara don a samu ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Yace Ita harkar gwamnati akwai maganar kudin shiga akwai kuma maganar kudin da ake kashewa, don haka abin da ake a irin wannan yanayi shine sai a duba aga wadanne kofofi na barna za a toshe, domin akwai hanyoyi da yawa da gwamnati zata iya kawo gyara a kan irin barnar da ake yi”.

Ya ce “Da irin wannan mataki gwamnati ta bi, da ‘yan kasa sun yi murna, sannan sun kuma ji dadi domin kowa abin da yake so shi ne ya samu rayuwa mai kyau”.

Kwankwaso ya ce, bisa la’akari da irin arzikin da Najeriya ke dashi, ba sai anje an dauki wasu matakai da za su dada hargitsa tsarin tattalin arzikin kasar ba yace ya kamata Gwamnati ta janye wannan kari da tai.

Labarai Makamanta