Idan Na Fice Daga PDP Jam’iyyar Ta Mutu – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa idan ya fita daga jam’iyyar adawa ta PDP yau, babu yadda za’ayi su ci zabe a Shekarar 2023 dake tafe.

Wike ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida ranar Juma’a a garin Fatakwal babbar birnin jihar. Yace irin karfin da shi da abokansa ke da shi babu wanda ya isa ya raina su kuma jam’iyyar PDP na bukatarsu idan tana son nasara a 2023.

“Alkawarin da muka yi kawai shine ba zamu fita daga jam’iyyar ba. Idan muka fita daga jam’iyyar shin ka san irin illan haka?” “Idan na fita da jam’iyyar yau. Babu yadda za’ayi PDP ta ci zabe. Idan muka fita, zamu fita tare da jama’armu ne, shine gaskiyan magana.” “Shin kana tunanin idan mu gwamnoni biyar muka fita PDP ba zata ruguje ba?

Labarai Makamanta

Leave a Reply