Idan Ba A Dakile Yawan Haihuwa Ba Najeriya Za Ta Kasa Motsi Nan Gaba – Obasanjo

Rahotanni daga Birnin Abeakuta babban birnin Jihar Ogun na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce karuwar yawan mutane a Najeriya na iya zama matsala idan ba a sarrafa hakan da kyau ba, anan gaba.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne yayin da yake magana a wani taro a jihar Ogun ranar Lahadi, dangane da yadda matsaloli suke kara yawaita a Najeriya.

A farkon wannan watan, Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda ya kiyasta cewa yawan mutanen Najeriya ya haura miliyan 211.

Da yake mayar da martani, Obasanjo ya yi hasashen cewa idan ba a dakile yawan mutanen ba, Najeriya za ta zama kasa ta uku mafi girma a duniya a shekara ta 2050. Ya kara da cewa dole ne kasar ta rungumi “kula da yawan jama’a” cikin sauri domin dakile wani mummunan sakamako na karuwar yawan ‘yan kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce: “Mun tashi daga miliyan 120 zuwa sama da miliyan 200, mun kara adadin yawan Faransawa zuwa yawanmu, kuma idan muka ci gaba da yadda muke tafiya, nan da shekara ta 2050, za mu zama kasa ta uku mafi girma a duniya.”

“Idan muka ci gaba a haka, zuwa shekara ta 3000, za mu zama babbar kasa a duniya. Yanzu, me za mu yi don magance lamarin? Ta yaya za mu magance wannan yawan?

Da yake jayayya kan cewa yawan na iya zama wata kadara ko kuma jidali, dattijon ya ce idan har al’umma ba ta shirya tsaf ba to kasar za ta dandana kudarta a yanzu da kuma nan gaba, inda zata kasa yin dukkanin wani motsi.

“Abin da ya kamata mu yi shi ne ilmantuwa game da kula da yawan jama’a. Wasu mutane ba sa son ambatan tsarin iyali, amma duk abin da za ku yi, dole ne ku sarrafa yawanku don amfanin duk abinda ke zaune a cikin al’ummar ku.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply