Shugaba ?asa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ziyarar da yaje Birnin Landan yaje ne domin ya samu hutu sosai bayan ayyuka da ya yi ta fama dasu a Najeriya.
Cikin wata wasika da Buhari ya aika wa Shugaban Kasar Jordan, wadda Garba Shehu ya sanya wa hannu, wasikar ta bayyana cewa Buhari ya je hutu ne, ba ta bayyana cewa ba shi da lafiya ko ya je ganin likita ba.
Sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta bayar kafin tafiya da Buhari ya yi, ta ce zai yi makonni biyu a Landan sannan ya dawo gida.
Tafiyar ta sa ta hadu da bacin ran ‘yan Najeriya, wadanda su ke rika nuna fushin yadda Buhari ya tsallake ya bar kasar nan, a lokacin da likitocin kasar su ka shiga yajin aikin neman a biya su hakkokin su da gwamnati ta ki biyan su.
Bayan Buhari ya sauka Ingila dai ya hadu da fushin wasu gungun ‘yan Najeriya mazauna can, domin kuwa sun shafe kwanaki biyu su na zanga-kofar gidan Najeriya, inda su ka nemi ya koma Najeriya ya nemi magani kuma ya gyara asibitocin Najeriya.