Mai Girma Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Muhammad Bello Matawalle, ya tsige mai martaba Sarkin Maru, Abubakar Chika, bisa zargin ba da goyon baya ga ‘yan bindiga da cin amanar talakawan shi.
Hakazalika gwamnan ya kuma tsige shugaban gundumar Kanoma, Lawal Ahmed kan wannan laifin da ake zarginsu da shi cikin gaggawa ba tare da ?ata lokaci ba.
Kungiyar tuntu?a ta magabatan arewa, ACF ta jinjinawa gwamnan game da irin matakin da ya dauka kan magoya bayan ‘yan bindiga.
Kakakin kungiyar ta ACF, Emmanuel Yawe, ya ce matakin da gwamnan ya dauka ya dace. A cewar Yawe, an dakatar da sarkin da hakimin tun a watan Yunin 2020 yayin da ake kan bincike.
Ya ce an same su da laifin ne bayan korafe-korafen da talakawansu suka yi na cewa suna hada kai da ’yan bindiga da masu satar mutane.
Kungiyar ta ce: “Mu a matsayin mu na Dattawan Arewa muna taya gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Mutawale murnar daukar wadannan kwararan matakan.”Allah Madaukaki wanda ba ya barci zai kiyaye shi. Babu abin da zai same shi.
”A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ‘yan Najeriya za su sha mamaki idan aka ba su labarin wadanda ke da hannu wajen sace ‘yan mata ’yan makaranta sama da 300 daga Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe.
An ruwaito cewa Matawalle ya yi wannan bayanin ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da Sarakuna 17 a jihar suka kai masa ziyarar jajantawa kan sace daliban.