Hukuncin Kisa Ne Ga Duk Wanda Ya Yiwa Ƙaramar Yarinya Fyaɗe A Musulunci – Daurawa

Sanannen Malamin addinin Musulunci a tarayyar Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewar doka a shari’ar Musulunci ta tanadi kisa ne ga dukkanin wanda ya aikata fyade ga ƙaramar yarinya.

Hakazalika shari’ar ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi amfani da wani makami wajen tursasa wata Mata da yi mata fyade.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana hakan ne a yayin da yake bada fatawa akan matsayin hukuncin fyade a musulunci da gidan rediyon BBC ya yi dashi.

Malamin ya ƙara da cewa idan kuma da amincewar mace aka yi mata fyade to wannan za’a yi ma wanda ya aikata fyaden hukuncin laifin zina ne, idan yana da aure a kashe shi, in kuma saurayi ne ayi mishi Bulala 100.

Sheikh Daurawa ya cigaba da cewar dukkanin wadannan hukunce hukuncen na ƙunshe ne bisa ga ijima’in malamai na ƙasar Saudiyya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply