Fitaccen dan Fim din nan wato Ali Nuhu ya fusata da matsalar tsaron da ya addabi yankin Arewacin Nijeriya, inda ya caccaki hukumomin tsaron kasarnan bisa gaza shawo matsalar tsaron da ake fuskanta musammana Arewacin Nijeriya.
Ali Nuhu ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook mai suna Ali Nuhu Mohammed inda ya ce; “wannan al’amari na rashin tsaro ya dade da wuce Misalin, hakika in har akwai hukumomin tsaro a kasar nan to sun tabbata marasa amfani”.
Inda ya ci gaba da cewa; “saboda kullum maimakon al’amari nan ya yi baya sai gaba ya ke. Shin abin tambaya anan shi ne, al’umar kasar ne ba damu da kare rayukansu da dukiyoyin su ba ko kuma rashin sanin makamar aiki ne?’ ya tambaya.
Abin da ya wallafa a shafinsa na Facebook
A ranar Asabar ne aka samu rahotannin da ke cewa wasu da ake tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki kuma suka kashe fiye da mutum 40 ta hanyar yi musu yankan rago, lamarin da ya harzuka ‘yan Nijeriya suke ta tofin Allah tsine ga gwamnatin kasar, tare da sabunta kiran ganin an yi watsi da shugabannin hafsoshin tsaron Nijeriya.