Hukumar Yaƙi Da Rashawa Ta Bankaɗo Badaƙala A Shirin Ciyar Da Yara

Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta (ICPC), a ranar Litinin, ta ce ta bankado makuden kudi har N2.67 biliyan na ciyar da ‘yan makaranta amma a asusun bankuna masu zaman kansu.

ICPC ta ce kudin da aka waskar zuwa asusun bankuna masu zaman kansu, an bada ne domin ciyar da yara ‘yan makaranta amma kuma suna gida.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin taron gangami a kan yaki da rashawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Farfesa Owasanoye ya ce an bankado N2.5 biliyan wanda babban ma’aikaci a ma’aikatar gona ya killace domin kansa.

Hukumar ta kara da bayyana cewa, ta samu wasu gine-gine 18, farfajiyar kasuwanci 12 da filaye 25, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Ya ce cibiyoyin gwamnati 33 ne suka yi bayani a kan N4.1 biliyan da aka tura ta TSA, N4.2 biliyan kuwa har yanzu babu bayani.

Labarai Makamanta

Leave a Reply