Hukumar WAEC Ta Fitar Da Jadawalin Zana Jarrabawa

Hukumar shirya jarrabawar kammala karantun sakandire ta Yammacin Afrika, WAEC, ta fidda jadawalin jarrabawar shekarar 2020.

Babban jami’in hukumar WAEC a Najeriya, Mista Patrick Areghan, shi ne ya bayyana a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin kasar na tarayya wato Abuja.

Ya tunatar da manema labarai yadda annobar korona ta wajabta dage jarrabawa wadda a baya aka kudiri gudanar da ita a tsakanin ranar 6 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Yuni.

Ya ce a halin yanzu bayan bita kan halin da ake ciki, za a gudanar da jarrabawar cikin tsawon lokacin da bai wuce makonni biyar ba, daga ranar 3 ga watan Agusta zuwa 4 ga watan Satumba.

Mista Patrick ya ce za rika gudanar da jarrabawar tun daga ranar Litinin har zuwa Asabar domin samun damar kammala ta cikin makonni biyar. Ya ce dalibai 1,549,463 ne suka yi rajistar zana jarrabawar a bana daga makarantu 19,129, inda 786,421 suka kasance maza yayin da kuma 763,042 suka kasance mata.

Ya gargadi dukkanin makarantu da dalibai da su guji duk wasu ababe na satar jarrabawa tare da cewa rashin aiwatar da kyakkyawan shiri ba zai taba zama uzuri na yi saba wa doka ba.

A karshe ya sanar da cewa, an aika da jadawalin karshe na jarrabawar bana ga ofisoshin hukumar na yankuna da rassa daban-daban da kuma ma’aikatun ilimi na gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply