Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya koka kan rashin isassun kuɗaɗe a hukumar.
Marwa ya bayyana cewa a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar, daga gidansa ya dauko Talabijin zuwa ofis, domin samun saukin gudanar da ayyuka.
Marwa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan miyagun kwayoyi domin kare naira biliyan 38 na kasafin kudin hukumarsa.
Shugaban Hukumar ya fada ma kwamitin cewa hukumar wacce ke da karfin ma’aikata 10,000 da sansanoni 173 a fadin kasar baya ga hedkwata, tana samun naira miliyan 33 duk wata don gudanar da ayyukanta.