Hukumar Kwastam Ta Yi Nasarar Kama Tulin Kakin Soji Da Na ‘Yan Sanda

Rahoton dake shigo mana daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Hukumar Kwastam ta yi nasarar kame wasu tufafin sojoji da na ‘yan sanda da aka shigo dasu kasar.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an kama kayan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, kamar yadda BBC ta ruwaito. A cewar rahoto, an yi fasa-kwabrin kayan ne daga kasar Afrika ta Kudu kuma sun shigo ne ba bisa ka’ida ba.

Mai magana da yawun hukumar Bello Kaniyal Dangaladima ne ya bayyana hakan ga kafar labaran, inda ya bayyana dalla-dalla kayayyakin da aka kwato.

A cewarsa, daga cikin kayayyakin da aka kwato sun hada da riguna, hulunan kwano na sojoji da kakin ‘yan sanda irin na Najeriya. Baya ga kayan na jami’an tsaro, an kama wasu miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol na masu darajar Naira biliyan 37. Ana kyautata zaton an shigo da miyagun kwayoyin ne daga kasar Pakistan da Indiya, kuma ana ci gaba da bincike a kai. Wannan babban kamu dai nasara ce ga kwastam, kuma ya zo daidai lokacin da kasar nan ke shirin babban zaben 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply