Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Kori Manyan ‘Yan Sanda

Hukumar kula da rundunar ‘yan sanda ta amince da korar manyan jami’an ‘yan sanda 10 tare da ragewa wasu 9 mukami. Kazalika hukumar ta amince da shawarar zartar da hukunci mai tsanani a kan wasu jami’ai 8 tare da bawa wasu jami’ai uku takardar gargadi.

Hukumar ta wanke wasu jami’ai uku da ake zargi da aikata laifi a yayin da ta amince da dakatar da albashin wasu jami’ai 10 a matsayin horo.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Ikechukwu Ani, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ya fitar ranar Juma’a.

Hukumar ta yanke wadannan shawarwari ne yayin zaman darektocinta, wanda aka yi ranar Talata, 28 ga watan Satumba, a Abuja karkashin jagorancin Shugaba Musliu Smith, tsohon sifeton rundunar ‘yan sanda.

“Yayin zaman, an tattauna a kan tuhumar zargin aikata laifuka da ake yi wa jami’ai 43. “Daga cikinsu, Hukumar ta amince da korar wani mataimakin kwamishina (ACP), jami’ai biyu ma su mukamin SP, jami’ai uku ma su mukamin DSP da kuma jami’ai hudu ma su mukamin ASP.

“Kazalika Hukumar ta bayar da umarnin gurfanar da wasu manyan jami’ai 6 da suka hada da; ACP , SP, DSPs biyu, da ASPs biyu,” a cewarsa.

Ya bayyana sunayen jami’an da abinda ya shafa kamar haka; jami’an 10 da aka kora,

ACP Magaji Ado Doko,

SP Ogedengbe Abraham,

SP Mallam Gajere Taluwai,

DSP Okunkonin Daniel,

DSP Abisoro Obo Irene,

DSP Theresa Nuhu (mai ritaya).

Sai ASP Sanusi Rasaki,

ASP Uwadala Ehis Oba,

ASP Ferdinand Idoko, da ASP Igolor Godsent Ogheneruona.

Jami’an da aka ragewa mukami sune kamar haka; Muhammad Sani Muhammad daga CSP zuwa SP,

John Oluwarotimi daga SP zuwa DSP.

Sai Godwin Agbo da Hassan Hamidu daga DSP zuwa ASP

Sai kuma Edeke Michael da Iyanda Olufemi wadanda aka ragewa mukami zuwa Insifekta daga ASP.

Labarai Makamanta