Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Hukumar INEC Ta Yi Gargadin Faruwar Rikici Gabanin Babban Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce yana fargaba game da ?aruwar kai hare-hare yayin da ?asar ke shirya wa babban za?en ?asar a watan Fabrairu mai zuwa.

Ana dai fargaba game da yiwuwar samun tashin-tashina a za?en na ba?i wanda ake ganin zai yi zafi.

Yakubu ya ce hukumar za?en ta gano cewa an samu hare-hare 50 masu ala?a da za?en a cikin watan farko na fara ya?in neman za?e.

Shugaban na INEC ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da hukumar ta kira bayan kai wa ofisoshinta biyu farmaki.

A Najeriya dai gwamnati na ci gaba da yun?urin ganin sun magance matsalolin tsaro da ke addabar ?asar, wa?anda suka ha?a da na masu i?irarin jihadi da kuma na ?an bindiga masu garkuwa da mutane.

A wani labarin na daban Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ?asar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matu?ar muhimmanci a guji tayar da hankula.

A wata sanarwa da fadar shugaban ?asar ta fitar a ranar Juma’a, shugaban ya nemi ?an ?asar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ?asar da Amurka da Birtaniya ke ?auka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.”

Wannan magana ta shugaban ?asar na zuwa ne a yayin da hankula ke ci gaba da tashi kan batun tsaro a Najeriya, tun bayan garga?in da Amurka da wasu ?asashen yamma suka yi cewa akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a ?asar.

“Najeriya ba ita ka?ai ce ?asashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ?an ?asashensu shawarar tafiye-tafiye ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai garga?in ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin daka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.

“An da?ile hare-hare. Jami’an tsaro ne banka?o barazanar da ake fuskanta don tsaron ?an ?asa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana bu?atar sirri.

“Zaman lafiyar ?an Najeriya shi ne mafi ?ololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.

Exit mobile version