Hukumar INEC Ta Yi Gargadin Faruwar Rikici Gabanin Babban Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce yana fargaba game da ƙaruwar kai hare-hare yayin da ƙasar ke shirya wa babban zaɓen ƙasar a watan Fabrairu mai zuwa.

Ana dai fargaba game da yiwuwar samun tashin-tashina a zaɓen na baɗi wanda ake ganin zai yi zafi.

Yakubu ya ce hukumar zaɓen ta gano cewa an samu hare-hare 50 masu alaƙa da zaɓen a cikin watan farko na fara yaƙin neman zaɓe.

Shugaban na INEC ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da hukumar ta kira bayan kai wa ofisoshinta biyu farmaki.

A Najeriya dai gwamnati na ci gaba da yunƙurin ganin sun magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da na masu iƙirarin jihadi da kuma na ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.

A wani labarin na daban Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Juma’a, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.”

Wannan magana ta shugaban ƙasar na zuwa ne a yayin da hankula ke ci gaba da tashi kan batun tsaro a Najeriya, tun bayan gargaɗin da Amurka da wasu ƙasashen yamma suka yi cewa akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a ƙasar.

“Najeriya ba ita kaɗai ce ƙasashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ƴan ƙasashensu shawarar tafiye-tafiye ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai gargaɗin ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin daka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.

“An daƙile hare-hare. Jami’an tsaro ne bankaɗo barazanar da ake fuskanta don tsaron ƴan ƙasa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana buƙatar sirri.

“Zaman lafiyar ƴan Najeriya shi ne mafi ƙololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply